IQNA

Iran Ta Bayyana Damuwa Kan Matsalolin Da Ake Haifar Wa Kasar Lebanon

17:55 - October 15, 2021
Lambar Labari: 3486428
Tehran (IQNA) ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana damuwa kan matsalolin da ake kokarin haifar wa kasar Lebanon.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sa’id Khatibzadeh ya bayyana muhimmancin kiyaye zaman lafiya da nustuwan da ake da shi a kasar Lebanon.
 
Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Khatibzadeh ya na fadar haka a yau Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, ya na fatan mutane da sojojin kasar Lebanon tare da kungiyar Hizbullah zasu ci gaba da kasancewa tare don magance matsaloli da fitinun da Haramtacciyar kasar Isara’ila take son tayarwa a kasar.
 
Daga karshen kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya mika ta’ziyyarsa ga gwamnati da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu a kisan da aka yiwa masu zanga-zangar lumana a birnin Beirut a jiya Alhamis. Sannan ya bukaci gwamnatin kasar ta kama wadanda suka aikata kisan ta kuma hukuntasu.
 
Mutane bakawai ne suka yi shahada a yayinda wasu kimanin sattin suka ji rauni a jiya Alhamis, a lokacin da wasu yan bindiga daga kan benaye masu tsawo suka yi barin wuta kan masu zanga-zangar lumana, ta neman a sauke wani alkalin da aka nada don binciken fashewar da ta auku a tashar jiragen ruwa na Beirut a shekarar da ta gabata.
 

 

 

 

captcha