IQNA

An Kai Hari A Babban Masallacin Juma'a Na Mabiya Mazhabar Shi'a A Garin Qandahar Na Kasar Afghanistan

19:43 - October 15, 2021
Lambar Labari: 3486429
Tehran (IQNA) an sake kai wani harin ta'addanci a masallacin Juma'a na mabiya mazhabar shi'a a garin Qandahar na kasar Afghanistan.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, wani bam ya tashi a cikin wani masallaci a lokacin da ake sallar juma’a a birnin Kandahar na kudancin kasar Afganistan a yau, rahoton ya ce akalla 15 ne suka rasa rayukansu a yayin da wasu kimanin talatin suka samu raunuka.
 
Kakakin ma’aikatar cikin gida na gwamnatin Taliban ya bayyana cewa mai yuwa yawan wadanda suka rasa rayukansu ya kara yawa saboda mummunan halin da wasu da suka ji rauni suke ciki.
 
A makon da ya gabata ma kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a wani masallacin ‘yan shi'a a ranar juma’a a garin Kundus na arewacin kasar, inda mutane kimani 150 suka rasa rayukansu wasu da dama suka ji rauni.
 
Nimatullahi Wafa tsohon dan majalisar dokokin lardin Kandahar ya bayyana cewa harin na yau ma, an kai shi ne cikin masallacin ‘yan shia a lokacinda suke sallar juma’a a cikinsa.
 

4005097

 

Abubuwan Da Ya Shafa: garin Qandahar ، kasar Afghanistan ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha