IQNA

Alhuthi: Gwagwarmaya Domin kare Kasa Daga Harin Makiya Wajibi Ne Na Addini

19:30 - October 19, 2021
Lambar Labari: 3486447
Tehran (IQNA) Abdulmalik Alhuthi shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana gwagwarmaya domin kare kasa daga makiya a matsayin wajibi na addini.

Tashar Almasirah ta bayar da rahoton cewa, a  cikin jawabin da ya gabatar na murnar zagayowar lokacin Maulidin manzon Allah (SAW) Abdulmalik Alhuthi shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana gwagwarmaya domin kare kasa daga makiya a matsayin wajibi na addini.

Al-Huthi ya kara da cewa wajabi ne ga mutanen kasar Yemen su yaki wadanda suka mamaye kasarsu don yin hakan wani jihadi ne a kan tafarkin Allah madaukakin sarki.

A cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne gwamatin kasar Saudiya da kawayenta da kuma Amurka suka aukawa a kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansu Hadi kan kujerar shugabancin kasar, bayan ya yi murabus sakamakon matsin lambar al'ummar kasar.

Yanzu an doshi kusan shekaru bakawai kenan Saudiyya na jagorantar kai munanan hare-hare kan al'ummar kasar Yemen ad sunan yaki da kungiyar Ansarullah da aka fi sani da kungiyar Alhuthi, amma har yanzu ba su iya murkushe kungiyar ba, a maimakon hakan sai kisan fararen hula da suke yi da rugurguza kasar.

4006185

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha