IQNA

Hamas Ta Yaba Wa Malaysia Kan yin Watsi Da Batun Kulla Alaka Da Isra'ila

21:46 - October 21, 2021
Lambar Labari: 3486457
Tehran (IQNA) Hamas ta yaba da matsayin da kasar Malaysia ta bayyana na goyon bayan al-ummar Falasdinu.

Kungiyar Hamas ta falasdinawa masu gwagwarmaya don kwatar ‘yancin falasdinawa ta yaba da matsayinda kasar Malaysia ta bayyana na goyon bayan al-ummar Falasdinu, bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bada sanarwar cewa nan ba da dadewa ba kasar Malaysia za ta shiga cikin wadanda za su kulla alaka da ita.

Kungiyar ta Hamas ta sanar da haka ne yau Alhamis a cikin wani bayanin da ta fitar, inda ta yaba wa Saifuddin Abdullahi ministan harkokin wajen kasar Malaysia wanda ya fito fili ya karyata labarin da yahudawa suka bayar.

Inda ya ce, kasar Malaysia ba za ta taba barin al-ummar falasdinu ba, kuma za  ta ci gaba da goyon bayan su har zuwa samun nasara a kan yahudawa yan mamaya.

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha