IQNA

Ayatullah Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr, Masanin Mai Kokarin Haɗa Kan Musulmi

Tehran (IQNA) Ayatullah Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr babban malamin addini ne wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada ilimi da neman hadin kan al'ummar musulmi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, a wani bangare na jawabinsa dangane da Ayatullah Shahid Sayyid Muhammad Baqir Sadr, yana fadar cewa: Marigayi Sadr (Allah Ya kara masa yarda) ya kasance ko shakka babu mai hazaka, abin da zai iya yi ba dukaknin malamai masana da masu tunani ne za su iya yinsa a fagage da dama.

Mutum ne wanda ya karar da rayuwarsa baki daya wajen yi wa addinin Allah hidima da kuma yada ilimi a tsakanin musulmi, da kare musulunci daga farmakin makiya a aikace ta hanyar kafa hujjoji na ilimi.