IQNA

Rashin Hadin Kan Musulmi Yana Da Tasiri Wajen Rura Wutar Kiyayya Da Musulunci A Duniya

21:38 - October 26, 2021
Lambar Labari: 3486478
Tehran (IQNA) Ismail Bukasa wakilin jami'ar Mustafa (A.S) a kasar Kongo ya ce Idan babu hadin kai na hakika a tsakanin musulmi, kyamar addinin musulunci za ci gaba da karuwa a duniya.

Ismael Bukasa wakilin jami'ar kasa da kasa ta Kongo (AS) kuma mai fafutukar kare hakkin bil'adama, a hirarsa da IQNA a gefen taron kasa da kasa kan hadin kan musulmi karo na 35, ya bayyana muhimmancin hadin kai tsakanin musulmi.
Ya yi nuni da illolin rarrabuwar kawuna da rashin hadin kai a tsakanin musulmi, inda Ya ce wajibi ne musulmi su kasance masu hadin kai na hakika da juna kan batutuwa daban-daban.
 
Bukasa ya kara da cewa: "Zan iya cewa rarrabuwar kawuna da rashin hadin kai zai raunana Musulmi, kuma wannan lamari zai shafi dukkan musulmi." Don haka wajibi ne dukkan musulmi su yi kokarin tabbatar da hadin kai na hakika a tsakaninsu.
 
Ya ce yana da kyau musulmi Ahlus-Sunnah da Shi'a su tsaya tsayin daka tare da taka rawa wajen ci gaban Musulunci da yaduwarsa, ba tare la'akari da banbancin fahimta ba, domin akida daya ta imani da Allah da manzonsa da kur'ani ta hada su.
 
Dangane da kyamar Musulunci da kuma irin rawar da hadin kan musulmi ke takawa wajen yakar wannan mummunar dabi'a ta zamantakewa, Bokasa ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin musulmi inda ya ce: "Idan har ba a samu hadin kai na hakika a tsakanin musulmi ba, kiyayya da Musulunci za ta rika karuwa kowace rana a duniya, kuma a karshe za ta yi mummunar illa ga Musulmi a wasu bangarori na duniya da suke rayuwa.
 

 

4007271

 

 
 
Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha