IQNA

Yahudawa Sun Rufe Masallacin Annabi Ibrahim (AS) A Birnin Alkhalil Da Ke Falastinu

17:33 - October 31, 2021
Lambar Labari: 3486495
Tehran (IQNA) yahudawa sahyuniya sun rufe masallacin Anabi Ibrahim (AS) da ke garin Alkhalil a cikin Falastinu.

Sheikh Hafizi Abu Asnina daraktan kwamitin masallacin Ibrahimi ya sanar da cewa, sojojin yahudawan sahyoniya sun rufe masallacin ga musulmi da sunan bikin yahudawa tare da barin sahyoniyawa mazauna masallacin su shiga cikin masallacin.

Ya kara da cewa: An rufe masallacin ne daga karfe 3 na yammacin ranar Juma'a 28 ga watan Nuwamba, kuma wannan wuri mai tsarki ya kasance a rufe ga Falastinawa masu ibada.

Abu Asnineh ya ci gaba da cewa: Rufe masallacin ya hada da hana kiran salla, sannan kuma an ba wa sahyoniyawa 'yan mamaya damar halartar masallacin da kuma gudanar da bukukuwansu.

A shekara ta 1972, hukumomin Isra'ila sun ba Yahudawa damar yin ibada a wata kusurwa a cikin masallacin.

Bayan kisan kiyashin da yahudawan sahyuniya suka yi wa musulmi a shekarar 1994, inda aka kashe masu ibada 29 tare da jikkata wasu daruruwa, masallacin ya kasu kashi biyu, na musulmi da yahudawa.

Isra'ila ba ta barin musulmi su yi addu'a ko kiran salla a cikin masallaci a lokutan bukukuwan Yahudawa.

Kimanin yahudawa 'yan sahayoniya 400 da ke zaune a cikin tsohon ginin  Hebron,  sojojin Isra'ila 1,500 ne ke gadin su.

 

4009306

 

captcha