IQNA

14:18 - November 10, 2021
Lambar Labari: 3486536
Tehran (IQNA) Hukumomi a jihar sun ayyana zaman makoki na kwanaki uku, biyo bayan iftila’in gobara data auku a wata makarantar renon yara da ta yi ajalin yara 25.

Hukumomi a jihar Maradi dake kudancin Jamhuriyar Nijar, sun ayyana zaman makoki na kwanaki uku, biyo bayan iftila’in gobara data auku a wata makarantar renon yara da ta yi ajalin yara 25.

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta sanar yayin taron majalisar ministocinta ta ce yara 25 ne suka rasu a gobarar, kana wasu 14 suka jikkata ciki har da biyar dake cikin mawuyacin hali.

Tuni gwamnatin kasar ta haramta amfani da azuzuwa zana a cikin kananan makarantu a duk fadin kasar.

Ko a watan Afrilu da ya gabata sama da yara ashirin ne suka rasa rayukansu a irin wannan gobara a wata makarantar yara a Yamai babban birnin kasar.

A wani labarin kuma mutum fiye da talatin ne suka rasa rayukansu biyo bayan ruftawar wata mahakar zinari ta gargajiya a garin Dan Isa dake jihar Maradi.

4012036

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: asa rayuka ، mahakar zinari ، zaman makoki ، kananan makarantu
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: