IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allawadai Da Gallazawar Da Yahudawa Suke Yi Wa Falastinawa

16:18 - November 11, 2021
Lambar Labari: 3486541
Tehran (IQNA) majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da yadda yahudawa suke gallaza wa Falastinawa.
Kwararun Majalisar Dinkin Duniya, sun fitar da wani sabon rahoto wanda a cikinsa sukayi tir da yadda yahudawa ke ci gaba da gallaza wa Falasdinawa a yankunan da suka mamaye a cikin wannan shekara.
 
Rahoton ya kuma soki gwamnatin Isra’ila kan rashin tabuka komai wajen shawo kan farmakin da ake kaiwa Falasdinawan, kamar yadda yarjejeniyar Geneva ta tanada.
 
A cikin rahoton kwararun sun bayyana cewa, maimaikon Isra’ila ta dauki mataki na kawo karshen lamarin, jami’an tsaronta na maida martani ta hanyar daukar matakin neman Falasdinawa su fice daga yankunansu.
 
Hare-hare 410 ne  yahudawa suka kai wa Falasdinawa a cikin wannan shekara da muke ciki, a cewar rahoton kwararun.
 
Wannan adadin ya karu idan aka kwatanta da bara inda aka samu hare hare 358, sai kuma 335 a shekarar 2019.
 
Kuma farmakin da ake kaiwa falasdinwan a yankunansu da Isra’ila ta mamaye, na shafar iyalai ne dake rayuwa a kauyuka da karkara dake yamma da kogin Jordan da Isra’ila ke ci gaba da mamayewa.
 
Kwararun na MDD, sun bukaci kasashen duniya dasu dauki mataki kan wannan cin zarafi da Isra’ila ke wa falasdinawa.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4012101
captcha