IQNA

17:50 - November 12, 2021
Lambar Labari: 3486545
Tehran (IQNA) Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, yunkurin da Saudiyya ke yi domin ganin ta haifar da yakin basasa a cikin kasar Lebanon ba zai taba yin nasara ba.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa kasashen larabwa da suke gaggawar kulla dangantakar diflomasiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila ba zasu iya kare ta daga kungiyoyi da kasashen da suke gwagwarmaya da ita a yankin gabas ta tsakiya ba, daga ciki har da kungiyar Hizbullah, idan har yaki ta barke a tsakaninsu.
 
Tashar talabijin ta Al-Manar ta kungiyar ta nakalto Sayyid Nasarallah ya na fadar haka a jiya Alhamis a lokacinda yake jawabi don tunawa da ranar shahidar ta kungiyar, wato 11 ga watan Nuwamba na ko wace shekara.
 
Sayyid Nasarrala ya kara da cewa saboda albarkan jinin shahidan kasar, kasar Amurka ta kasa samun iko da gwamnatin kasar Lebanon. Haka ma sauran kasashen yankin wadanda suke sun zama suna da fada a ji a cikin harkokin kasar Lebanon.
 
Daga karshen Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa kokarin da gwamnatin kasar Saudiya take yi na dawo da yakin basasa a kasar Lebanon ba zai taba samun nasara ba.
 
Dangane da kasar Yemen kuma, ya ce ya kamata Saudiya ta san cewa Kungiyar Hizbullah da Iran ba zasu tattauna da ita a madadin mutanen kasar Yemen ba, idan tana son zaman lafiya ta dauke takunkuman tattalin arziki na zaluncin da ta dorawa kasar ta Yemen sannan ta shiga tattaunawa kai tsaye da su.

4012437

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: