IQNA

Cikar Shekara Guda Da Rasuwar Babban Makarancin Kur'ani A Masar

20:48 - November 20, 2021
Lambar Labari: 3486584
Tehran (IQNA) Sheikh Abu al-Wafa al-Sa'idi ya kasance daya daga cikin manyan makarantun kur'ani mai tsarki a Masar da kuma duniyar musulmi, wanda ya rasu shekara guda da ta wuce yana da shekaru 64 a duniya.

A jiya Juma'a ne ake tunawa da rasuwar daya daga cikin manyan makarantun kur'ani mai tsarki a kasar Masar da kasashen larabawa, Qari Mahmoud Abu al-Wafa al-Saeedi, wanda ake yi wa lakabi da "Muryar Dutse" ya rasu a ranar 19 ga Nuwamba, 2018 yana da shekaru 64.
 
An haifi Sheikh Mahmoud Abu al-Wafa al-Sa'idi a shekara ta 1954 a kauyen Kalh al-Jabal da ke lardin Aswan, kuma kamar sauran yaran kauyen, mahaifiyarsa ta yi sha'awar danta ya haddace kur'ani mai tsarki, musamman ma tun da yake Mahaifiyarsa ta kasance malamar haddar Alqur'ani ga yaran kauye.
 
Ya fara haddar Alkur'ani tun yana dan shekara hudu, sannan ya je wajen Sheikh Muhammad Abu al-Ala da Sheikh Kamal ya kammala haddar Alkur'ani.
 
Shaharar da Sheikh Mahmoud Abu al-Wafa al-Sa'idi ya yi, ya sa ya bar ayyuka da dama na kyautata zamantakewa a rukunin Tahrir da karatun Alkur'ani mai girma.
 
Abu al-Wafa al-Sa'idi ya shiga gidan rediyon a matsayin makranci a shekara ta 1371 kuma ya yi karatu a karon farko a shekara ta 1374 daga masallacin Sayyeed Zainab (AS).
 
Sheikh Mahmoud Abu al-Wafa al-Sa'idi ya yi ziyararsa ta farko zuwa kasar Holland, sannan ya je kasashe da dama domin halartar tarukan kur'ani da kuma gabatar da tilawa.
 

4014782

 

 

 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Holland ، kasashe ، tilawa ، shekara ، makaranci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha