IQNA

Australia Ta Saka Kungiyar Gwagwarmaya Ta Hizbullah A Cikin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda

15:01 - November 24, 2021
Lambar Labari: 3486599
Tehran (IQNA) Gwamnatin Australia, ta sanya gabadayan kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon a jerin kungiyoyin da take kallo a matsayin na ‘yan ta’adda.

Tunda farko dai matakin ya tsaya ne ga bangaren soji na kungiyar, wadda take da karfin fada a ji a kasar ta Lebanon.

Babu wani dalili da kasar ta bayar na daukar wannan matakin, amma a cewar ministar cikin gida ta kasar, Karen Andrews, ta ce kungiyar gwagwarmayar dake samun goyan bayan Iran, na ci gaba da zama barazana da kuma goyan bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Amurka da Isra’ila dai sun jima da ayyana kungiyar Hezbollah a matsayin ta ‘yan ta’ada, amma wasu kasashe sun ki sanya bangaren siyasa na kungiyar a cikin jerin ‘yan ta’adda saboda fargabar kada hakan ya dagula musu alaka da hukumomin kasar Lebanon.

Sanya kungiyar a jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda na nufin haramta Hezbollah a kasar da kuma hana duk wani matum  gudanar da harkoki da ita a kasar ta Australiya inda ‘yan Lebanon da dama ke da zama.

 

 

4015786

 

captcha