IQNA

Hamas Ta Yi Allawadai Da Saka Hizbullah Cikin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda Da Australia Ta Yi

16:23 - November 25, 2021
Lambar Labari: 3486604
Tehran (IQNA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kakkausar suka kan kiran da kungiyar Hizbullah ta Lebanon a matsayin kungiyar ta'addanci da Australia ta yi.
A cikin sanarwar, kungiyar Hamas ta bayyana kiran kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta ta'addanci da gwamnatin kasar Australia ta yi, hakan yana a matsayin wata alama ta mika kai ga matsin lambar gwamnatin yahudawan sahyoniyawa, da kuma goyon bayan laifukan da take aikatawa kan al'ummar musulmi da na larabawa da suka hada da Lebanon, Siriya da Palastinu.
 
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar yada labaran Falasdinu ta bayar da rahoton cewa: Kungiyar Hizbullah ta yi tir da gwamnatin mamaya tare da gudanar da ayyukanta na keta hakkin bil adama, da addini, da kuma ayyukanta kan kisan gillar da ta ke yi.
 
Sannan Hizbullah ta ce matakin an Australia ba iya hana ta ci da kare al'ummar kasar Lebanon  daga zaluncin yahudawan sahyoniya ba.
 
Bangarori daban-daban daga sassa daban-daban na kasashen larabawa da na musulmi suna ci gaba da yin tir da Allawadai da wannan mataki an Australia a kan Hizbullah, wanda yake nuni da cewa Australia ta mika kai ga matsin lamba daga iyayen gidanta.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4016230
captcha