IQNA

21:51 - November 25, 2021
Lambar Labari: 3486606
Tehran (IQNA) Hukumar zaben kasar Iran ta ce an kammala sake kidaya kuriun da aka kada a zaben 'yan majalisa.
Hukumar zabe a kasar Iraki ta bada sanarwan cewa ta kammala aikin sake kirga kuri’u a mazabunda wasu yan takara na wasu jam’iyyu a kasar suka yi korafin an yi masu magudi, suka kuma bukaci a sake irgen kuri’un da aka kada da hannu a mazabun nasu.
 
Kamfanin dillancin labaran WAA na gwamnatin kasar ta Iraki ya nakalto hukumar zaben kasar tana cewa a yau Alhamis ta kawo karshen sake kirga kuri’un da aka kada a mazabun da aka gabatar da korafi a kansu, a gaban wadanda suka yi korafi ko wakilansu, ko wakilan jam'iyunsu. Har'ila yau hukumar zaben ta ce sakamakon sake kirgen ya yi dai 100% da na na’urorin komfuta wanda hukumar ta bayar bayan an kammala zaben na watan jiya.
 
Kafin haka dai wasu ‘yan takara sun yi korafin an yi masu magudi, kuma dole ne hukumar zaben ta sake kirgen kuri’u a mazabunsu da hannu ido na ganin ido.
 
An gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Iraki ne a cikin watan Oktoba da ya gabata ta hanyar amfani da na’urorin komfuta a karon farko a kasar.
 
https://iqna.ir/fa/news/4016105
Abubuwan Da Ya Shafa: hukumar zabe ، majalisar dokoki ، kasar Iraki ، korafi ، amfani
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: