IQNA

19:35 - November 30, 2021
Lambar Labari: 3486624
Tehran (IQNA) An dage taron hadin kan Musulmi ta Duniya da za a yi a wata mai zuwa a Abu Dhabi sakamakon bullar wani sabon nau'in cutar korona a wasu kasashe.

Kamar yadda shafin jaridar The National News ya ruwaito, shugaban kwamitin shirya taron Ali Rashed al-Nuaimi, ya ce an yanke hukuncin ne saboda wasu mahalartan ba za su iya komawa kasashensu ba idan aka kebe su.

"Duk da cewa kasar UAE da ke karbar bakuncin taron wannan sabon nau'in corona na Omicron bai shafe ta bay a zuwa yanzu, amma matakan da aka dauka a wasu kasashen na iya haifar da keɓancewa tare da yin wahala ga baƙi komawa ƙasashensu," in ji shi.

An shirya taron kasa da kasa kan "Hadin kai na Musulunci: mai taken “Ra'ayoyi, Dama, Kalubale" a ranar 12-14 ga Disamba na wannan shekara.

 

4017178

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: zaman taro ، hadin kan musulmi ، wannan shekara ، keɓancewa ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: