IQNA

Mahaifi Da Dansa Suna Karatun Kur'ani Mai Tsarki Tare

Tehran (IQNA) A cikin sabon sakonsa a yanar gizo, Mahdi Gholamnejad tare da daya daga cikin ‘ya’yansa, suna karanta Suratul Balad.

Mahdi Gholamnejad fitaccen makarancin kur'ani ne na kasa da kasa daga kasar Iran, wanda ya saka sabon sako a shafinsa na yanar gizo yana karatu tare da dansa.