IQNA

Mahalarta Gasar Kur'ani Ta Duniya Sun Fara Isa Birnin Alkahira Na Kasar Masar

23:42 - December 09, 2021
Lambar Labari: 3486665
Tehran (IQNA) Rukunin farko na mahalarta gasar kur’ani ta kasa da kasa karo na 28 a Masar sun isa birnin Alkahira a daren jiya.

Shafin yada labarai na sadal Balad ya bayar da rahoton cewa, A daren jiya ne rukunin farko na 'yan kasashen waje da za su halarci gasar kur'ani ta kasa da kasa karo na 28 da za a  gudanar a kasar Masar suka fara isa birnin Alkahira daga kasashen Larabawa da na Musulmi daban-daban, inda suka sauka a wani otal a birnin Alkahira domin halartar gasar da za a fara ranar Asabar 11 ga watan Disamba.

Mohammad Tariq al-Ansari da Minhaj Ahmed daga Indiya da Nazar Sultan Bai daga Kazakhstan da aka shirya za su fafata a gasar Harshen Larabci na daga cikin mahalartan kasashen waje.
 
An shirya gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 28 a kasar Masar daga ranar 11 zuwa 15 ga Disamban 2021.
 
Kashi na farko na wannan gasa shi ne haddar Alkur’ani baki daya ta hanyar karantawa da fahimtar ma’anar ayoyi da harshen Larabci.
 
Fage na biyu shi ne haddar Alkur’ani baki daya tare da Tajwidi ga maza da mata wadanda ba sa jin harshen Larabci, matukar dai shekarun mahalartan bai wuce shekara 30 ba.
 
Fage na uku shi ne haddar kur’ani mai tsarki ga masu bukata ta musamman – ‘yan kasar Masar kawai – matukar shekarun mahalartan bai wuce shekaru 30 ba.
 
https://iqna.ir/fa/news/4019656
 
 
 
 
captcha