IQNA

'Yan Bindiga Sun Kashe Masallata A Jihar Neja Da Ke Najeriya

23:41 - December 10, 2021
Lambar Labari: 3486668
Tehran (IQNA) A Najeriya, Wasu Mahara ‘dauke da Manyan Bindigogi sun Auka wa wasu mutane da ke Sallar Asubahi a garin Ba’are a Karamar Hukumar Mashegu a jihar Neja dake Arewacin kasar, inda akalla Mutane sha shida suka mutu.

A rahoton da gidan rediyon Faransa ya bayar, ‘Yan bindigar sun kai harin ne a Asubahin wayewar garin jiya Alhamis.

Har ya zuwa lokacin hada rahoton ba a sami wani bayani ba daga Gwamnatin jihar Nejan ba, sai dai kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Monday Bala Kuryas wadda ya tabbatar da kai hari ya ce Mutane 9 ne suka rasa rayukansu.

Wannan dai shine karo na 2 da ‘Yan bindigar suka kai irin wannan hari ga masu sallah a karamar hukumar Mashegun.

A kwanakin Baya ma ‘yan bindagar sun kashe Mutane 18 a dai dai lokacin da suke Sallar Asuban a garin Maza kuka dake yankin Mashegun.

4019874

Abubuwan Da Ya Shafa: jihar Neja ، Najeriya ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha