Taha Hassan al-Fashni fitaccen makaranci ne a kasar Masar wanda yake da sha'awar kwaikwayon karatun Sheikh Mustafa Ismail.
Daga cikin fitattun ayyukansa da suka raye akwai Ibtihalin yabon ma'aiki da ahlul bait na "Hub Al-Hussein", "Ya Iha Al-Mukhtar" da "Milad Taha". A daidai lokacin da ake tunawa da zagayowar lokacin rasuwarsa, za mu wani bangare na karatunsa daga surat Ibrahim: