IQNA

An Gudanar Da Sallar Rokon Ruwa A Masallacin Harami Da Kuma Masallacin Ma'aiki (SAW) A Madina

21:24 - December 14, 2021
Lambar Labari: 3486683
Tehran (IQNA) Dimbin masu ziyara a dakin Allah mai alfarma da ke Makka da masallacin Annabi da ke Madina ne suka gudanar da sallar rokon ruwan sama.

Tashar Alakhbar 24 ta bayar da rahoton cewa, Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa alihi Sallam ya koyar game da yin sallah a lokacin da aka samu jinkirin damina, a safiyar jiya ne masallata daga sassa daban-daban na kasar Saudiyya suka gudanar da sallar rokon ruwan sama.

A birnin Makkah, an gudanar da sallar rokon ruwan sama a Masallacin Harami, karkashin jagorancin Abdul Rahman bin Abdul Aziz Al-Siddis, babban daraktan Masallacin Harami da Masallacin Annabi.

A cikin hudubar sallar rokon ruwan sama, Abdurrahman Sudais ya yi kira ga mutane da kada su yanke kauna daga rahamar Ubangiji.

A madina, jama'a da dama sun gudanar da sallar rokon ruwan sama a masallacin Annabi bisa ka'idoji na kiwon lafiya da kuma kiyaye tsafta.

Tun da farko dai Sarkin Saudiyya Salman ya bukaci al'ummar kasar da su gudanar da addu’oi a lokacin sallar la'asar a sassa daban-daban na kasar a jiya Litinin.

 

 

4020644

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha