IQNA

An Samar Da Manhajar Kur’ani Da Harsuna Da Dama A Saudiyya

17:13 - December 15, 2021
Lambar Labari: 3486687
Tehran (IQNA) Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Saudiyya ta sanar da kaddamar da manhajar kur'ani mai girma da yaruka da yawa.

Shafin yada labarai an hamrain News ya bayar da rahoton cewa, Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Saudiyya ta sanar da kaddamar da manhajar kur'ani mai girma da yaruka daban-daban a cikin salon kira’ar da ta zo a ruwayar "Warsh".

A cewar ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Saudiyya, wannan manhaja ta kur'ani mai tsarki cibiyar buga kur'ani mai tsarki da ke Madina ta samar da ita,  kuma tana aiki a kan manhajojin Apple, Windows da Android.

Rahoton ya ce, an yi amfani da na’urar “Mushaf na Warsh” ne don amfanin na’urori da wayoyin salula domin biyan bukatun musulmi da suke karatun kur’ani bisa ruwayar Warsh.

 

4021040

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: manhaja ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha