IQNA

Taron Tunawa Da Cika Shekaru 1100 Da Zuwan Musulunci A Tatarstan

22:37 - December 15, 2021
Lambar Labari: 3486688
Tehran (IQNA) A shekara mai kamawa za a gudanar da manyan shirye-shirye na tunawa da shekaru sama da dubu na Musulunci a Tatarstan.

Shafin Asia News ya bayar da rahoton cewa, Mataimakin firaministan Jamhuriyar Tatarstan na kasar Rasha Marat Khosnulin ya amince da shirye-shiryen bikin cika shekaru 1,100 da musuluntar 'yan kabilar Volga na Bulgariya.

A cikin shekarar 2022 mai kamawa, an shirya abubuwan 71, Abu mafi muhimmanci shi ne gina wani katafaren masallaci a Kazan, babban birnin Jamhuriyar Tatarstan, mai suna Babban Masallacin Suburnaya.

Ginin zai hada da gidan tarihi, dakin karatu da kuma wurin nuna abubuwa da dama na addini.

Har ila yau, za a kaddamar da wasu ayyukan a cikin biranan Ulyanovsk da Nizhny Novgorod da kuma a Moscow fadar mulkin tarayyar Rasha.

Bugu da kari kuma, za a bude wata cibiya ta kimiyya ta nazari da buga rubuce-rubucen muslunci a Kazan, kuma za ta kasance a bude ga masu bincike da sauran jama'a.

An kuma shirya taruka da dama masu taken "Rasha da Duniyar Musulunci"  tare da halartar wakilan Kungiyar Hadin Kan kasashen musulmi OIC, Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki ta Kazan da UNESCO, wanda kwamitin tarihi na duniya ne zai dauki nauyin gudanar da taron karo na 45 a Kazan.

4021199

 

captcha