IQNA

Zaman Makokin Ranakun Shahadar Fatima Zahra (AS) A Bishkek

22:40 - December 18, 2021
Lambar Labari: 3486700
Tehran (IQNA) Masoya da mabiya tafarkin Ahlul Baiti (AS) sun gudanar da zaman makoki a masallacin Imam Ali (AS) da ke birnin Bishkek babban birnin kasar Kyrgyzstan, domin tunawa da zagayowar ranakun Fatimiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da taron ne a jiya 17 ga watan Disamba tare da halartar jama'a da dama da suka yi juyayi.
 
Ruwayoyi da nazarce-nazarce kan ranar shahadar Sayyida Fateeh Zahra (a.s) sun banbanta, saboda haka ne aka yi la’akari da kwanaki na shahadar Sayyida Zahra (AS) kuma tsakanin kwanakin biyu ana kiransu da ranaku na Fatimiyya.
 
A bisa kalandar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a yau 27 Azar, daidai da 13 Jamadi-al-Awal, ita ce ranar da ake tunawa da ita matsayin ranar shahadar Sayyida Zahra (AS) .
 
 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: shahadar Sayyida Zahra ، kwanaki biyu ، zagayowa ، Fatimiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha