IQNA

Masallatan Malaysia Na Karbar Bakuncin Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Raba Da Muhallansu

19:29 - December 20, 2021
Lambar Labari: 3486709
Tehran (IQNA) Masallatan Malaysia sun karbi bakuncin dubban mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Kuala Lumpur da sauran jihohin kasar.

Kamfanin dillancin labaran barnama ya bayar da rahoton cewa, masallatai a Kuala Lumpur da Putrajaya sun bude kofofinsu domin tsugunar da dubban mutanen da mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa suka raba da muhallansu.

 
Ministan kula da harkokin addini na kasar Idris Ahmed ya sanar da daukar matakin bude kofofin manyan masallatai ga wadanda ambaliyar ta shafa a ranar Lahadi 19 ga wannan wata  naDisamba.
 
Ya ce Masallatan a shirye suke kuma za su ba da taimakon da ya kamata, da hakan ya hada da abinci da abin sha da sauran kayayyakin bukatar rayuwa na gaggawa, da kuma layuka na internet.
 
Ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama da aka yi a kasar Malaysia ya raba mutane sama da 15,000 da muhallansu, tare da rufe hanyoyi da dama da kuma dakile jigilar kayayyaki.
 
Sama da ‘yan sanda, sojoji da jami’an kashe gobara 66,000 ne aka tattara a duk fadin kasar domin taimakawa wajen ceto wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da kuma kwashe su zuwa wurare masu aminci.
 
 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha