IQNA

Gwamnatin Indiya ta rufe masallacin tarihi mafi girma a Jammu da Kashmir

21:27 - December 23, 2021
Lambar Labari: 3486719
Tehran (IQNA) Gwamnatin Indiya ta rufe babban masallacin Srinagar da ke Jammu Kashmir a wani mataki na murkushe musulmi.

Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, Wannan masallacin na tarihi an gina shi shekaru sama da 600, kuma ya kasance daya daga cikin muhimman cibiyoyi na ilimin addinin musulunci a Jammu da Kashmir tsawon shekaru aru-aru.

Bangarori da dama a Indiya sun yi Allah wadai da matakin, inda ake ganin rufe masallacin a matsayin saba wa ikirarin da gwamnatin Firayim Minista Narendra Modi ta yi na kare hakkin bil'adama da 'yancin addini.
 
Gwamnatin Modi dai ta yi ikirarin cewa masallacin ya kasance wurin zanga-zanga da kuma fadace-fadacen da ke barazana ga tsaron yankin Kashmir da ake takaddama a kansa, don haka ya kamata a rufe shi.
 
A watan Janairun da ya gabata, gwamnati ta yanke shawarar katse layukan tarho da intanet a yankin, inda Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama da suka hada da Human Rights Watch suka yi Allah wadai da matakin na gwamnatin Indiya.
 
Kungiyar ta bayyana cewa gwamnatin Indiya ta dauki matakin ne saboda tsoron fallasa take hakkin dan Adam da ake yi wa 'yan kasar Musulmi a yankin Kashmir.
 
Mazauna yankin na Kashmir da musulmi ke da rinjaye sun nemi shiga Pakistan tun bayan da Indiya ta sami ‘yancin kai a shekarar 1947.
 
A ranar 5 ga Agusta, 2019, Gwamnatin Indiya ta soke doka ta 370 na Kundin Tsarin Mulki; Wanda yake  tabbatar da cin gashin kan yankin Jammu da Kashmir. A halin yanzu an raba yankin zuwa manyan sassa biyu, wanda gwamnatin tarayya ke tafiyar da su.
 

 

 

captcha