IQNA

Saudiyya na Ci Gaba Da Kara Tsananta Hare-Harenta A Kan Al'ummar Kasar Yemen

22:47 - December 26, 2021
Lambar Labari: 3486733
Tehran (IQNA) jiragen yakin gwamnatin Saudiyya na ci gaba da kara tsananta hare-harea akn biranen kasar Yemen.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, jiragen yakin gwamnatin Saudiyya na ci gaba da kara tsananta hare-hare a akan biranen kasar Yemen.

Kakakin majalisar koli ta gudanarwa da ayyukan jin kai na kasar Yamen Talar Al sharjabi ya fadi cewa sojojin kasar Saudiya sun kai hari da gangan kan Asibitoci da wajen cunkoson jama’a, kuma ya bayyana shi a matsayin laifin yaki da zai kara jefa alummar kasar cikin mawuyacin hali.

A nasa bangare babban daraktan kula da lafiyar jam’a a birnin Sana’a Mutahar Al- Marwani ya fadi cewa harin da Saudiya ta kai kan Asibiti ganganci ne domin kawai ta kara matsin lamba kan kasar da lalata bangaren kiwon lafiya na kasar, da yanzu haka ya tabarbare sakamakon yakin da saudiya ta kaddamar akan kasar

A ranar juma'a ce jiragen yakin Kasar Saudiya suka yi wani lugudan wuta kan wani Asibiti a babban birnin kasar Yemen Sana’a da hakan ya haddasa mummunar asara, tare da kashe mutane uku dukkanin fararen hula da suka hada da jariri daya, kamar yadda a yau Lahadi sun kai wasu munanen hare-hare makamantan wannan a wasu sassan birnin.

 

4023359

 

 

captcha