IQNA

Dalilin Da Yasa Jakadan Japan A Saudiyya Yake Son Sauraron Karatun Kur’ani Mai Tsarki

21:13 - December 27, 2021
Lambar Labari: 3486739
Tehran (IQNA) Fumio Iwai, jakadan kasar Japan a kasar Saudiyya, ya bayyana karfafa harshen larabci a matsayin dalilin da ya sa yake sha’awar kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, Jakadan kasar Japan ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi 26 ga watan Disamba cewa, ya fara sauraron kur’ani mai tsarki, musamman surar Fatiha, da zimmar karfafa fasahar harshen Larabci.

Jami'in diflomasiyyar na Japan ya dogara kacokaf akan Twitter don samun alaka da Miliyoyin 'yan kasar Saudiyya ne ke binsa a shafinsa na Twitter. Hotunansa da bidiyoyinsa na rayuwar yau da kullum a Saudiyya sun samu karbuwa a wajen masu sauraronsa.

Ya ce a halin yanzu yana sauraron wasu bangarorin na kur'ani da yadda ake karanta su, domin ayoyin kur'ani larabci tantagaryarsa da ba shi da hadi da wani karen harshe na wata kabila daga cikin kabilun kasashen larabawa, hakiaknin larabcin zallansa.

 

4023791

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha