IQNA

Harsuna 21 Ne Kamfanin Dillancin Labaran IQNA Ke Watsa Labarai Da Su A Halin Yanzu

18:33 - December 29, 2021
Lambar Labari: 3486746
Tehran (IQNA) Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a daren jiya ne aka bude shafin yanar gizo na na harshen Portugal a matsayin harshen na ashirin da daya na wannan kafar yada labarai, tare da halartar Mustafa Rostami shugaban ofishin Jagora a bangaren jami'o'i.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, an bude bangaren harshen Portuguese a matsayin harshe na 21 na kamfanin dillancin labaran kur'ani na kasa da kasa, a daren jiya a wajen baje kolin nuna ayyuka da nasarorin da aka samu a jami'oin Iran, tare da halartar Hojjatoleslam Mustafa Rostami Wakilin Jagora a jami'o'i, da Mohammad Hossein Hassani, shugaban kamfanin dillancin labaran iqna.

Mostafa Rostami ya ziyarci baje kolin nuna ayyuka da kuma kwarewa da nasarorin da jami'oi suka samu, inda ya duba rumfar IQNA da kuma cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar.

Kaddamar da harsunan IQNA ya samo asali ne daga kwarewar da wannan kafar yada labarai ta samu ne da kuma bayyana bukatun musulmi da yanayin da suke ciki a kasashen duniya  da bayar da cikakkun labarai da rahotanni masu amfani ga musulmi a cikin harsuna daban-daban.

jimlar mutane miliyan 270 ke magana da harshen Portuguese ko dai a matsayin harshen kasa na farko, ko kuma harshensu na biyu, musamman wasu daga cikin kasashen da Portugal ta yi wa mulkin mallaka.

Wannan yare Harshen hukuma ne a ƙasashe tara da suka haɗa da Portugal, Brazil, Mozambique, Angola, Guinea-Bissau, Timor-Leste, Equatorial Guinea, Cape Verde, Sao Tome da Principe, Har ila yau ana yaren Portuguese a Macau.

4020508

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha