IQNA

Azhar Ta Mika Sakon Sabuwar Shekara Miladiyya Ga Mabiya Addinin Kirista

18:49 - December 31, 2021
Lambar Labari: 3486762
Tehran (IQNA) Ahmed al-Tayyib, Sheikh al-Azhar, ya wallafa a shafinsa na Twitter yana taya kiristoci a fadin duniya murnar Kirsimeti da kuma shiga sabuwar shekara.

Sheikh Al-Azhar a cikin wani sako ga Paparoma Francis shugaban mabiya darikar Katolika na duniya yana cewa; "Paparoma Tawadros II", shugaban Kiristoci 'yan Koftik a Masar; Justin Welby, Archbishop na Cocin Canterbury; Shugabannin coci-coci da na Kirista a Gabas da Yamma muna taya ku murnar shiga sabuwar shekara da Kirsimeti.
 
Ahmed al-Tayyib ya wallafa sakon taya murnarsa a shafukansa na sada zumunta da harsuna shida da suka hada da Ingilishi da Larabci da Faransanci da Italiyanci da kuma Turkiyya.
 
“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba mu zaman lafiya da soyayya da ‘yan uwantaka a duniya, ya kuma tseratar da mu daga yaki da kiyayya,” inji shi.
 
 

4024980

 

 

 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: zaman lafiya ، a duniya ، ‘yan uwantaka ، harsuna ، Ingilishi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha