IQNA

An Sheka Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya A Masallacin Haramin Makka Mai Alfarma

17:12 - January 02, 2022
1
Lambar Labari: 3486769
Tehran (IQNA) An sheka Ruwan sama kamar da bakin kwarya a Makka da Masallacin Harami a lokacin da masu ziyara ke gudanar da ayyukan ibada.

Tashar Russia Today ya bayar da rahoton cewa, masu ziyara a dakin Allah da Umrah sun shaida ruwan sama kamar da bakin kwarya a Makka da Masallacin Harami a yammacin yau 2 ga watan Janairu.

Duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya, mahajjatan Umrah sun ci gaba da gudanar da ayyukan tawafi da na Umrah.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun ba da labarin farin ciki da jin dadin Umrah da masu ibadar a  Masallacin Harami ta hanyar yada hotunan wannan ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Babban daraktan kula da yanayi da kare muhalli na kasar Saudiyya ya sanar da ci gaba da samun ruwan sama a yankunan arewaci da kuma yankin Makkah.

4025374

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Shin dama haka ya taba faruwa koko a'a?
Shin wannan shine karon farko na ruwan Sama a harami ko dama anayi?
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha