IQNA

An Sanar Da Lokacin Ganin Watan Ramadan A Wasu Kasashen Larabawa

18:16 - January 04, 2022
Lambar Labari: 3486779
Tehran (IQNA) Masana falaki sun sanar da lokavin ganin jinjirin watan Ramadan a wasu kasashen Larabawa wanda zai kasance a ranar 2 ga Afrilu, 2022.

Masana falaki sun sanar da cewa: Watan Ramadan na shekara ta 1443 Hijira - idan aka ga jinjirin wata - ana sa ran zai fara ne a ranar 2 ga Afrilu, 2022 .
 
Ana kuma hasashen cewa watan Ramadan mai zuwa zai cika kwanaki 30 kuma zai kare a yammacin Lahadin daya ga watan Mayu 2022.
 
Ibrahim Al-Jarwan, shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar masana falaki ta Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma memba na kungiyar kasashen Larabawa ta sararin samaniya da falaki, ya bayyana cewa saura kwanaki 90 a shiga watan Ramadan mai alfarma, Don haka, bisa kididdigar ilmin taurari, ranar Asabar 2 ga Afrilu, ita ce farkon watan Ramadan mai alfarma.
 
Kwamitin Shari’ar Musulunci da ke da alaka da Darul Ifta na kasar Masar ya kuma sanar da cewa a ranar 1 ga Afrilu, 2022, kwamitin zai fara dubar jinjirin watan Ramadan, amma an yi hasashen cewa ranar 2 ga watan Afrilu ce za ta zama ranar farko ta ramadan a kasar Masar.
 
Dangane da ranar da za a gudanar da Sallar Idi, kwamitin ya kuma bayyana cewa, domin ganin jinjirin watan Shawwal, kwamitin zai fara duba jinjirin watan Shawwal a ranar daya ga watan Mayun shekarar 2022.
 

4026129

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha