A yayin ganawar, Sarki Abdallah ya jaddada wajabcin wanzar da cikakken zaman lafiya a yankunan Palasdinawa, da daukar dukkan matakan da suka dace don samun cikakken zaman lafiya bisa tsarin samar da kasashe biyu masu cin gishin kansu.
Dangantaka tsakanin Jordan da gwamnatin sahyoniyawan a karkashin tsohon Firaminista Benjamin Netanyahu (2009-2010) ta sukurkuce, inda har sarki Abdallah ya bayyana tu a matsayin "mafi muni" a wata ziyara da ya kai Amurka.
Hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan Masallacin Al-Aqsa da kuma wuraren ibadar musulmi a Falasdinu, ya haifar da kara tabarbarewar dangantaka a tsakanin bangarorin biyu, bayan da Jordan ta bayyana hakan a matsayin keta hakkin da take da shin a kula wuraren Falasdinawa da ke gabashin birnin Quds, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tababtar da hakan a cikin wani kudiri a shekaru baya.