IQNA

Shugaban Majalisar Kuwait ya jaddada ci gaba da goyon bayan Falasdinu

18:16 - January 09, 2022
Lambar Labari: 3486798
Tehran (IQNA) Marzouk al-Ghanim ya yaba da irin tsayin dakan da mutanen Kudus suke da shi kan wuce gona da iri na yahudawan sahyuniya, yana mai jaddada yadda Kuwait ke ci gaba da goyon bayan al'ummar Palastinu wajen kare hakki nasu.

Gwamnatin kasar Kuwait na ci gaba da yin tsayin daka a kan matsayinta, na amincewa da dokar da ta ayyana yahudawan sahayoniya a matsayin 'yan mamaya a Falastinu da kuma rashin halascin gwamnatin da suka kafa, wanda kuma wannan doka an amince da ita ne a shekarar 1967," a cewar majalisar dokokin Kuwait a wani taron kungiyar matasa kan birnin Kudus domin yin nazari kan ci gaba da yin riko da matakin da Kuwait ta dauka kan batun Falasdinu.

Yayin da yake mai cewa dokokin Palastinu da tsaronta ba su canza ba, shugaban majalisar dokokin Kuwait ya ce: Sake gabatar da shirin takunkumin da Isra'ila ta yi a majalisar dokokin kasar ba wani sabon abu ba ne, sai dai ya tabbatar da tsayuwar da Kuwait ta dauka na goyon bayan Falasdinu.

Shugaban majalisar dokokin kasar Kuwait ya kuma yi tsokaci kan matsayin tawagar Kuwaiti a gaban tawagar Isra'ila a zaman taro na 337 na majalisar dokokin kasar Kuwait da aka gudanar a watan Oktoban shekarar 2017 a birnin St. Petersburg na kasar Rasha. Tawagar Kuwait ta bukaci a kori wakilan gwamnatin sahyoniyawan daga taron.

"Wasu 'yan adawar siyasa sun kai mana hari kan matsayinmu a Rasha," in ji al-Ghanim. Duk da haka, a wasu lokuta muna iya samun sabani, amma ba mu sami sabani kan batutuwa kamar goyon bayan Falasdinu ba.

Bugu da kari, Al-Ghanem ya yaba da irin tsayin dakan da al'ummar Quds suka yi kan wuce gona da iri da gwamnatin  sahyoniya ta yi a kan Quds Sharif da Masallacin Al-Aqsa; A cikin sakon da ya aike wa mutanen Kudus ya ce: Nasara ta wannan hanya za ta tabbata.

Shugaban majalisar dokokin Kuwait ya kammala da cewa: Gwamnati da al'ummar kasar Kuwait na daga cikin manyan masu goyon bayan gwamnatin Palasdinawa a dukkanin kungiyoyin kasa da kasa da tarukan tarurrukan kasa da kasa, kuma suna ganin cewa batun Palastinu shi ne mafi muhimmanci a kasashen Larabawa.

 

 

4027231

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha