IQNA

Koyar Da  Al-Qur'ani Ga 'Yan Mata A Masallacin Kazemin

15:38 - January 11, 2022
Lambar Labari: 3486805
Tehran (IQNA) Cibiyar kur'ani mai tsarki ta hubbaren Kazemin ta shirya wani shiri na musamman na kur'ani ga 'yan matan Iraki.

Cibiyar kur’ani mai tsarki mai alaka da sashin kula da al’adu na haramin Kazemin ta gudanar da wani shiri na musamman ga ‘yan mata domin karfafa al’adun addini a wannan bangare na al’umma a harabar Haramin Imam Kazem (AS).

Wannan shiri na kur'ani ya kunshi bangarori na addini, al'adu da kuma karantar da sallah, horaswa kan yadda ake yin alwala da sauran abubuwa.

Haka kuma an gabatar da jawabai kan shirin, inda suka bayyana mahimmancin ayyukan addini da karfafa gwiwar 'yan mata wajen sanya hijabi.

A cewar masu gudanar da wannan shiri, an kafa wannan aiki na ilimi da nufin tallafawa yara mata da karfafa ilimin kur’ani da kula da su bisa manufar sakatariyar hubbaren Kazemain, ta yadda za a iya isar da mahanga ta Musulunci a cikin tunanin 'yan mata a cikin al'umma; Domin 'yan mata su ne ginshikin samar da iyali da zamantakewa a cikin al'umma.

برگزاری دوره آموزش قرآن برای دختران عراقی در صحن حرم امامین کاظمین(ع) + عکس

برگزاری دوره آموزش قرآن برای دختران عراقی در صحن حرم امامین کاظمین(ع) + عکس

برگزاری دوره آموزش قرآن برای دختران عراقی در صحن حرم امامین کاظمین(ع) + عکس

 

4027774

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha