Kamfanin dillancin labarabn anatoli ya bayar da rahoton cewa, ya zuwa yanzu dai Akalla mutane 10 ne suka mutu sakamakon rugujewar gini mai hawa uku na coci a yankin Okpanam da ke Najeriya, kamar yadda kwamishinan lafiya na Najeriya Onunie Mordi ya bayyana a wata sanarwa.
Ya bayyana damuwarsa kan karuwar adadin wadanda suka mutu, yana mai cewa an ceto wasu mutane takwas kamar yadda rahotannin farko suka bayyana.
Ana ci gaba da aikin neman agaji da ceto a yankin, kuma ana jinyar wadanda suka jikkata a asibiti.
An ce sama da mutane 50 ne suka halarci cocin a lokacin da lamarin ya faru.