IQNA

22:05 - January 17, 2022
Lambar Labari: 3486833
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi kakkausar suka dangane da harin ta'addanci da aka kai a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Hussein Ibrahim Taha ya fitar, ya yi kakkausar suka kan wannan mummunan harin bam, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkata wasu da ba su ji ba ba su gani ba, a kasar Somaliya.

Ya kuma jajantawa iyalan wadanda harin ta'addancin ya rutsa da su da gwamnati da al'ummar Somalia, da yin addu’ar Allah ya ba wa wadanda suka jikkata lafiya.

Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi yayi Allah wadai da duk wani aikin ta'addanci tare da bayyana goyon bayansa ga kokarin gwamnatin Somaliya na yakar irin wadannan ayyuka.

Wata mota makare da bama-bamai ce ta tarwatse a kan ayarin motocin hukumar UNHCR a arewacin filin jirgin sauka da tashin jiragen sama na Mogadishu babban birnin kasar Somaliya a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 8 tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun ce kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

 

4028924

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Babban sakataren ، kungiyar hadin kan kasashen musulmi ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: