IQNA

Tilawar Majalisin Kur'ani Tsakanin Iraniyawa Da Irakawa

19:49 - January 19, 2022
Lambar Labari: 3486841
Tehran (IWNA) An fitar da wani faifan bidiyo na karatun wasu makaratun kur'ani na Iran da Iraki a intanet, inda su ke kokarin karfafa gwiwar masu sauraro wajen karanta ayoyin da suke karantawa.

A cikin wani fim da aka fitar na Sayyid Javad Hosseini, wani makarancin Iran da yake karatu a daya daga cikin da'irorin kur'ani na Iran, mutane sun yi sha'awar karanta suratul Duha tare da shi.

Haka nan Meysam Tamar wani mai karatu dan kasar Iraqi yana karanta ayoyin Suratul Duha a hubbaren Husaini yana karanta su ta yadda mutane za su rika karanta ayar tare da shi.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4029492

captcha