IQNA

20:24 - January 19, 2022
Lambar Labari: 3486842
Tehran (IQNA) Kungiyar Taliban dake mulki a Afganistan ta yi kira ga kasashen musulmi dasu amince da gwamnatinta a Afghanistan.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, da yake sanar da hakan a wannan Laraba, fira ministan gwamnatin ta Taliban, ya ce lokaci ya yi da ya kamata kasashen musulmi su amince da gwamnatinsu a hukumance.

Mohammad Hassan Akhund, ya ce hakan zai taimaka wa Afganistan din samun ci gaba cikin sauri.

Mista Akhund, ya yi wannan furicin yayin wani taron manema labarai game da matsananciyar matsalar tattalin arziki da kasar ke fama da shi tun bayan zuwan gwamnatin ta Taliban a watan Agusta na bara.

Haka kuma kasar na fama da matsalar rashin samun agajin kasa da kasa, wanda ya jefa ‘yan kasar da dama cikin ukuba.

 

 

4029926

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: