IQNA

17:19 - January 20, 2022
Lambar Labari: 3486845
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya gana da Iraniyawa mazauna kasarRasha a ziyarar da yake kaiwa a kasar.

 A daren jiya shugaban Iran Ibrahim Ra’isi ya gana da Iraniyawa ‘yan kasuwa da kuma malaman jami’o’I gami da ma’aikata a bangarori daban-daban da suke a zaune a kasar Rasha.

Ganawar dai ta gudana ne a babban ginin ofishin jakadancin kasar ta Iran da ke birnin Moscow fadar mulkin kasar Rasha, inda ya karfafa gwiwarsu kan wajabcin yin aiki tsakaninsu da sauran takwarorinsu na cikin gida a kasar ta Iran, domin saun galaba a kan kalubale da ke a gaban kasar ta fuskoki daban-daban.

Ra’isi ya kai ziyara kasar Rasha ne da nufin karfafa alaka tsakanin kasar Iran da Rasha a dukkanin bangarori, inda a jiya suka yi doguwar ganawada shugaba Putin a birnin na Moscow.

Ra’isi da Putin sun jaddada cewa, alaka tsakanin kasashen Iran da Rasha, ta wuce batun kasuwanci da tattalin arziki kawai, alaka ce ta ta shafi dukkanin bangarori, kuma za su mayar da wannan alaka ta zama ta dogon lokaci bisa yarjejeniya a tsakaninsu da hakan zai hada har da bangaren ayyukan soji.

 

4030000

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: