IQNA

15:27 - January 22, 2022
Lambar Labari: 3486850
Tehran (IQNA) Hubbaren Imam Ali ya shirya wani taro na kur’ani  day a shafi  maulidin Sayyida Zahra (a.s) wanda wani bangare ne na tarukan kwanaki biyu na mata masu gudanar da ayyuka a bangaren kur'ani na kasar Iraki.

An fara gudanar da wannan taro ne a jajibirin zagayowar ranar haihuwar Sayyida Zahra (AS) kuma ana ci gaba da gudanar da shi har tsawon mako guda.

"Bikin ya hada da shirye-shirye na kur'ani da addini da na al'adu iri-iri wanda ya dauki tsawon mako guda," in ji Salim al-Jasani, mamba a majalisar gudanarwa a hubbaren Imam Ali kuma shugabar kwamitin shirya taron.

Ta kara da cewa: "Kafa da'irar Al-Qur'ani, bude dakin karatun kur'ani a tsangayar ilimin fikihu ta jami'ar Kufa, da gudanar da taron kur'ani a tsangayar ilimin 'yan mata na jami'ar Kufa da kuma gudanar da babban bikin makon  Tsaftace harabar hubbaren Imam (AS)  wani bangare ne na wannan biki."

Sannan kuma ta ce: Bude sabon ginin babban dakin karatu na jami'ar Al-Muthanna da ke kasar Iraki, da aikin ginin ofishin cibiyar Darul-Qur'ani ta  Ahlus Sunna a  yankin Diwaniyah na kasar Iraki wasu sassa ne na wannan bikin.

 

https://iqna.ir/fa/news/4030217

Abubuwan Da Ya Shafa: ilimin fikihu ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: