Ahmed Musa ya bayar da gudummawar dalar Amurka 1,500 ga babban masallacin garin Garoua, kuma mai taimaka wa Musa kan harkokin yada labarai ya tabbatar da hakan a wata hira da jaridar Muslim News.
Masallacin na kusa da sansanin ‘yan wasan Najeriya ne, kuma an yi amfani da shi wajen shirya ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afrika dake gudana a kasar Kamaru.
Za a kashe wadannan kudade ne wajen aikin gyaran Masallacin. A baya dai Ahmed Musa ya taba zama gwarzon shekara a kafar yada labarai ta Muslim News.
Ahmed Musa (an haife shi a watan Oktoba 14, 1992) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya wanda ya taka leda a Fanloo (Netherland), CSKA Moscow, Leicester City (Ingila) da Al Nasr a ƙasar Saudiyya.