IQNA

Makaranta Biyu daga Iraki sun kai matakin karse na gasar kur'ani ta kasa da kasa a Iran

23:12 - January 31, 2022
Lambar Labari: 3486890
Tehran (IQNA) Makaranata biyu daga kasar Iraki sun kai matakin karshe na gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 38 na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Yas Fadl, mai karatun kur’ani dan kasar Iraqi da Daniel Karim Ghazban, dalibin kasar Iraqi, sun samu nasarar zuwa matakin karshe na gasar kur’ani ta kasa da kasa ta Iran.

An gudanar da matakin share fage na gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 38 na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fannoni biyu na haddar kur'ani mai tsarki da kuma karatun kur'ani mai tsarki ta yanar gizo.

An zabo wadanda suka halarci gasar ne ta hanyar gasar kasa da kasa ta manyan makaranta kur'ani, wadda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasa ke gudanarwa duk shekara.

Wata mata mai haddar kur'ani mai suna "Zahra Abduljabbar" ita ma ta kai matakin karshe na gasar mata ta duniya a matsayin wakiliyar kasar Iraki a fannin haddar kur'ani mai tsarki baki daya.

 

 

4032602

 

captcha