
A cewar ofishin kula da harkokin addini na birnin Qudus, adadin masu ibada a masallacin Al-Aqsa a yau ya kai kimanin dubu arba'in.
Da sanyin safiyar yau ne dakarun gwamnatin sahyoniyawan suka hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa, yayin da suke gudanar da bincike da kuma duba takardun shaidar Palasdinawa.
Sojojin yahudawan sahyoniyawa 'yan mamaya sun warwatsu kan titunan birnin Quds da kewayen masallacin Al-Aqsa da kuma kusa da kofarsa, inda suka hana dubban masu ibada shiga masallacin.
Sai dai dubban al'ummar birnin Quds ne suka gudanar da sallar asuba a masallacin Al-Aqsa domin amsa gayyatar da jami'an Falasdinawa suka yi musu na halartar sallar jam'i, kamar yadda kuma kimanin mutane dubu arba'in sun iya samun damar yin sallar Juma'a a masallacin mai alfarma.
https://iqna.ir/fa/news/4033736