IQNA

Ana Shirin Fara Gasar Kur'ani Mai Tsarki Ta Duniya Ta Port Saeed Masar

22:04 - February 05, 2022
Lambar Labari: 3486912
Tehran (IQNA) ana shirin fara kaddamar da gasar haddar kur'ani karo na 5 ta kasa da kasa a lardin Port Said na kasar Masar.

Ana shirin fara kaddamar da gasar haddar kur'ani karo na biyar ta kasa da kasa a lardin Port Said na kasar Masar, tare da halartar firaministan Masar Mustafa Madbouli.

Adel Ghazban, gwamnan Port Said, ya sanar da cewa, hukuma ta kammala dukkan shirye-shiryen tunkarar gasar ta kasa da kasa, sannan ta bayyana adadin kasashe 66 da za su halarci gasar, da suka hada da na  Larabawa da na Afirka, da Turai, da kuma Amurka da Canada.

Ya ci gaba da cewa: “A yayin wannan gasa, wasu fitattun malaman addinin Musulunci guda uku, Ahmad Omar Hashem, mamba a majalisar manyan malaman Masar, Ahmad Naina, farfesa a fannin karatu da kuma Ridha Abdul Salam, shugaban gidan rediyon kur’ani mai tsarki a Masar, za su sanya ido kan gasar.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4033784

captcha