IQNA

Sayyid Nasrullah: Amurka Ummul Haba’isin Rikicin Ukraine

16:01 - March 02, 2022
Lambar Labari: 3487003
Tehran (QNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Nasrullah ya bayyana Amurka a matsayin ummul haba’isin rikicin kasar Ukraine.

Babban sakataren Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayani a lokacin bukin cika shekaru 30 da shahadar tsohon shugaban kungiyar Sayyid Abbas Musawi da Isra’ila suka yi masa kisan gilla, inda ya kara da cewa abin da ke faruwa a kasar Ukrain yanzu babban darasi ne ga wadanda suka aminta ko suka dogara da Amurka.
Har ila yau Sayyid Nasrullah ya yi gargadi cewa makomar rikicin Rasha da Ukrain yana da matukar hatsari ga duniya baki daya idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa a kasa.
Bayanan nasa yana zuwa ne bayan kalamai masu harshen damo da kafafen watsa labarai na kasashen turai suke yadawa kan rikicin rasha da Ukrain da ya jawo yin tir daga kasashen duniya.
Daga karshe ya sanya alamar tambaya game da irin matakin da duniya ta dauka lokacin da Amurka ta mamaye kasar Afghanistan da kuma wanda ta nuna bayan harin soji da kasar Rasha ta kai a kasar Ukraine, duniya tana girmama mai karfi ne kawai amma tana yin gum da baki kan laifukan da Amurka take tafkawa a kan kasashe masu rauni a duniya.
 
https://iqna.ir/fa/news/4039648
 

Abubuwan Da Ya Shafa: sayyid nasrullah lebanon hizbullah
captcha