Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Furat cewa, rundunar ‘yan sandan Karbala ta sanar da shirin tsaro na musamman na tarukan tsakiyar watan Sha’aban da kuma zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (A)
Fahim al-Kariti, kakakin rundunar ‘Operation Karbala’ ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan ta shirya wani shiri na musamman na tsaro ga masu ziyara a tsakiyar watan Sha’aban, wanda zai kasance cikin kwanciyar hankali ba tare da tsangwama ba.
Al-Kariti ya jaddada cewa, rundunar ayyuka na bukatar goyon bayan wasu rundunonin soji daga wasu larduna da kuma wasu sassan da ke taimakawa.
Ya bayyana cewa za a fara aikin ne kwanaki biyu kafin tsakiyar watan Sha’aban, kuma za a kammala shi ne da tashin maziyarta daga lardin Karbala.
A duk shekara a daidai lokacin da aka haifi Imam Mahdi (as) a birnin Karbala ana kawata hubbaren Imam Husaini (a.s) da furanni tare da kunna fitulu da dama albarkacin Imam Mahdi (as).
Haka nan kuma a wannan karon an kawata farfajiya da hubbaren Sayyidina Abolfadl Al-Abbas (AS) tare da kawata katangarsa da baranda, an rataye rubuce-rubucen kalmomi masu kyau a kan kofa da bango.
An kuma ajiye furanni da ciyayi na ado tare da rubutattun kalmomi na taya murna a mashigar farfajiyar mai alfarma da kofofinta.