IQNA

Malaman Indiya suna goyon bayan sanya hijabin 'yan matan Musulmi

21:15 - March 22, 2022
Lambar Labari: 3487081
Tehran (IQNA) Malamai a sassa daban-daban na Indiya sun bayyana goyon bayansu ga dalibai mata musulmi tare da kare hakkinsu na sanya hijabi a cikin aji.

A rahoton jaridar Times of India, malaman sun ce a  cikin wata sanarwa; "A matsayinmu na malaman makarantu da kwalejoji da jami'o'i a sassa daban-daban na Indiya, muna nuna goyon bayanmu ga 'yancin dalibai musulmi na sanya hijabi a cikin ajujuwa,"

Wannan yana nuna 'yancin kai na mata da tasirinsu, kuma hijabi ba ya kawo cikas ga ingancin ilimi ta kowace fuska.

A wani bangare na sanarwar, an bayyana cewa dalibai da dalibai na addinai daban-daban, ajin zamantakewa da jinsi kuma suna magana da harsunan uwa mabambanta; A lokacin karatun su, suna koyon tunani da bincike mai zurfi game da duniyar da ke kewaye da su; A cikin wannan tsari, ɗalibai wani lokaci suna jaddada imaninsu, wani lokaci kuma su keɓe su a gefe.

A ranar 15 ga watan Maris ne kotun kolin jihar Karnataka ta Indiya ta amince da dokar hana sanya hijabi a cikin azuzuwan jihar; Hukuncin a cewar masu lura da al’amura, sannu a hankali zai shafi sauran al’ummar kasar da ke da ‘yan tsiraru musulmi.

Dokar hana dalibai musulmi sanya hijabi a makarantu da jami'o'in jihar ya fuskanci tarzoma sosai daga su da iyayensu.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4044543

captcha