IQNA

16:12 - March 24, 2022
Lambar Labari: 3487086
Tehran (IQNA) A daidai lokacin da watan Ramadan ke karatowa mahardatan kur’ani mai tsarki 700 ne aka kammala yaye su a kasar Habasha. 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, mazauna kauyukan yankin Urmia na kasar Habasha sun shaida bikin yaye dalibai 700 da suka haddace kur’ani mai tsarki daga wata cibiya ta addinin musulunci mai suna Zayd bin Thabet.

Wani mai wa'azin kasar Habasha Sheikh Amin Ebru ya fitar da hotuna da bidiyo na bikin, inda ya nuna masu haddar kur'ani sun yi layi a cikin sahu suna tafiya a kan titunan kauyen domin murnarsu.

Wadannan mutane suna zuwa masallatai daban-daban don gudanar da tarukan ibada na musamman a wannan wata.

فارغ التحصیلی 700 حافظ قرآن در اتیوپی در آستانه ماه مبارک رمضان + فیلم  /// اماده

 

https://iqna.ir/fa/news/4044737

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: