IQNA

16:40 - April 01, 2022
Lambar Labari: 3487111

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya kan yawan mutanen da ke cikin kangin talauci a Yemen

Tehran (IQNA) Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan 25 da digo 5 a kasar Yemen na fama da talauci.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya kan yawan mutanen da ke cikin kangin talauci a Yemen

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta nakalto a shafinta na Twitter cewa, sama da mutane miliyan 25.5 daga cikin mutane miliyan 30 ne ke fama da talauci a kasar Yemen.

A saboda haka yakin kasar Yemen wanda ya faro shekaru 7 da suka gabata kuma yana ci gaba, ya kuma raba 'yan kasar Yemen miliyan 4 da muhallansu tare da hana yara sama da miliyan biyu ilimi.

An kuma bayyana cewa al'ummar Yemen na bukatar taimakonmu a yanzu fiye da kowane lokaci.

Saudiyya ta kaddamar da hare-haren soji kan kasar Yemen tare da killace kasar ta kasa da sama da ta ruwa tun daga ranar 26 ga Afrilu 2015, tana mai cewa tana kokarin dawo da tsohon shugaban kasar Yemen mai murabus a kan mulki.

Harin sojin Saudiyya bai cimma ko daya daga cikin manufofinsa ba har yanzu, sai dai ya kashe da raunata dubun-dubatar al'ummar kasar Yemen, da korar miliyoyin jama'a, da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma yaduwar yunwa da cututtuka masu masu hatsari.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4046036

 

captcha