A cewar India Today, shugaban jam’iyyar MNS Raj Takri ya ba da sanarwar cewa dole ne gwamnati ta yi hakan daga nan zuwa ranar 3 ga Mayu.
"Idan gwamnatin jihar ba ta cire lasifika daga cikin masallatai kafin ranar 3 ga Mayu ba, 'yan jam’iyyar MNS za su buga wakar Hindu (Hanuman Chalisa) a gaban masallatan," kamar yadda Takri ya fadawa wani gangamin magoya bayansa..
A farkon watan Afrilu, Raj Takri ya ba da sanarwar cewa ya kamata gwamnatin kasar India ta hana gabatar da jawabai da ake yi a dukkan masallatai, yana mai cewa masu jawabai na damun wasu.
Ya ce ba ya adawa da wata ibada, amma mutane su yi ibadarsu a wuraren da suke zaune, kada su takura ma wasu.
Bayan jawabin Raj Takri, da yawa daga cikin magoya bayan MNS sun fara yada taken adawa da musulunci a gaban masallatai, wanda ya kare da sa hannun 'yan sanda.
Raj Takri ya jaddada cewa idan har gwamnatin jihar ba ta dauki mataki ba, shi da ‘yan jam’iyyarsa ba za su dauki nauyin abin da zai biyo baya ba.
A baya dai an sha sukar Takri da jam'iyyarsa da yin amfani da tashin hankali a lokacin yakin neman zaben jam'iyyarsu, musamman kan bakin haure da kuma ‘yan tsiraru a kasar India.